(ABNA24.com) Rahotanni sun bayyana cewa kasashen turai uku wadanda aka fi sani da E3, wadanda kuma suka rattaba hannu a kan yerjejeniyar nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015, sun amince da cewa Amurka ba ta da hurumin tsawaita takunkumin hana Iran saya da seyar da makamai wanda ya zo cikin kudurin majalisar mai lamba 2231.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani jami’in diblomasiyyar tarayyar Turai yana fadawa tashar talabijin ta CNN kan cewa kasashen Jamus, Ingila da Faransa ba za su goyi bayan Amurka kan manufarta na tsawaita takunkumin saya da seyar da kamamai ga kasar Iran ba, wanda kuma zai kare a karshen wannan shekarar ba.
Majiyar ta kara da cewa, kawo karshen takunkumin, bangare ne na yerjejeniya nukliyar kasar Iran, wacce aka fi sani da JCPOA, don haka dagewa Iran takunkumin a karshen watan Octoba na wannan shekara wajibi ne.
Peter Stano kakakin kungiyar tarayyar Turai ya kara da cewa ‘kasar Amurka ta daina halartan tarurrukan yarjejeniyar ta JCPOA tun bayan ficewarta daga cikinta a shekara 2018.
Takunkumin ya fara aiki ne tun shekara ta 2006, kuma zai kare a cikin watan Octoba na wannan shekara ta 2020,amma Amurka tana son a tsawaitashi duk da cewa ta fice daga yarjejeniyar.
/129
Kasashen Turai Uku Sun Amince Kan Cewa Amurka Ba Ta Da Hurumin Tsawaita Takunkumin Makamai A Kan Iran
2 Mayu 2020 - 03:42
News ID: 1032222

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen turai uku wadanda aka fi sani da E3, wadanda kuma suka rattaba hannu a kan yerjejeniyar nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015, sun amince da cewa Amurka ba ta da hurumin tsawaita takunkumin hana Iran saya da seyar da makamai wanda ya zo cikin kudurin majalisar mai lamba 2231.